
Dan majalisar tarayya mai wakilatar kananan hukumomin Ajingi,/Albasu/Gaya, Dr Ghali Mustapha Tijjani ya kaddamar da rabon buhunan hatsi 18,600 ga al’ummar mazabarsa, domin tallafa musu a wannan lokaci na watan azumin Ramadan .
Da ya ke jawabi a wajen bikin kaddamar da rabon kayayyakin a Kano a jiya Juma’a, Panda ya ce ya yi hakan ne don sanya farin cikin a zukatan al’ummar mazabar sa musamman a wannan wata na Ramadan.
A cewarsa, idan aka yi la’akari da kalubalen tattalin arzikin da kasar nan take fama da shi, ba shi da wani zabi a matsayinsa na wakilin su da ya wuce ya raba wa al’ummar mazabar sa wasu kayan abinci da za su taimaka masu.
Ya bayyana cewa zai raba buhunan shinkafa 3,600 mai nauyin kilogiram 25 da kuma buhunan shinkafa 3,000 mai nauyin kilogiram 10.
Ya kara da cewa, buhu 6000 na garin masara mai nauyin kilogiram 10 da buhun gero 6000 wadanda suka an raba su ga al’ummar kananan hukumomi Gaya Ajingi da Albasu .
Panda ya kara da bayyana cewa, baya ga rabon kayan abinchin ya raba kudi naira miliyan 20 ga matasa 1000 wadanda suka fito daga wadancan kananan hukumomi, kuna yace wannan kashin farko ne nan gaba zai kara baiwa wasu irin wannan tallafin don inganta rayuwar su.
“Wannan somin tabi ne. Za mu ci gaba da irin wannan har tsawon shekarar nan.
“Za mu yi aiyukan raya ƙasa da zai shafi al’ummar mu ta Gaya da Albasu da Ajingi. Za mu tallafawa mata da matasa da bunƙasa harkar noma da lafiya da ilimi da yardar Allah,” in ji shi.
A jawabinsa tun da fari, mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara na musamman kan harkokin siyasa, Sunusi Surajo Kwankwaso, ya yabawa Panda bisa wannan aikin alkhairi da ya yi ga al’ummar sa.
Kwankwaso wanda ya wakilci gwamnatin jihar ya ce sabbin ‘yan majalisar musamman ‘yan jam’iyyar NNPP sun fi kowa kokari a tarihin Kano wajen kokarin taba rayuwar al’ummarsu.