Home Labarai Dan shekaru 57 ya yiwa kanwar mai dakinsa ciki

Dan shekaru 57 ya yiwa kanwar mai dakinsa ciki

0
Dan shekaru 57 ya yiwa kanwar mai dakinsa ciki

Daga Hassan Y.A. Malik

Wani mutum mai shekaru 57 da aka bayyana sunansa da Emmanuel ya gurfana a gaban kuliya a Abakaliki, babban birnin jihar ebonyi bisa zarginsa da dirkawa kanwar mai dakinsa ciki.

Matar Emmanuel ta bayyana cewa rikici ya fara cikin gidan aurensu ne a lokacin da kanwarta, IIjeoma Nwaokpuru, da ke zama a tare da su a cikin gidan ta yi batar dabo, amma daga bisani sai ta samu cewa mijinta ne ya karbawa kanwar tata gidan haya bayan da ya fahimci cewa tana dauke da cikinsa.

Ijeoma mai shekaru 17 ta bayyanawa manema labarai cewa, mijin yayarta ya ribace da alkawarirrika da dama dalilin da ya sanya ta aminta da bukatarsa na ya kwanta da ita.

A cewar Ijeoma, “A lokacin da ya bukaci da na zo mu yi, sai na ki amincewa da bukatarsa, amma da ya yi min alkawarin cewa zai bani kulawa ta musamman tare da daukar nauyin karatuna har na kammala jami’a, sai na amince.”

Shi ma Emmanuel, a jawabinsa ga manema labarai ya bayyana cewa abinda ya faru aikin shaidan ne.

“Ina son matata matuka, amma ban san abinda ya faru ba. Ina kyauatata zaton dai shaidan ne ya rinjayeni, saboda ni ba mutumin banza bane. Ina rokon mai dakina da ta yafe min, saboda a wannan hali da a ke ciki ma bani da karfin daukar nauyinsu su biyun,” inji Emmanuel.

Kotu ta umarci Emmmanuel da ya ci gaba da kulawa da Ijeoma, sannan ta daga sauraron karar zuwa gobe Juma’a, 23 ga watan Maris, 2018.