Home Ilimi Dan takara ya sanya yara 1,300 a makaranta a Kano

Dan takara ya sanya yara 1,300 a makaranta a Kano

0
Dan takara ya sanya yara 1,300 a makaranta a Kano

 

 

Wani ɗan takara a jihar Kano, Yusuf Abdullahi Da’awa, ya sanya yara, ƴaƴan marasa ƙarfi guda 1,300 a makaranta, tare da raba musu kayan karatu.

Da yanke jawabi a wajen taron ƙaddamar da shirin a yau Lahadi, Da’awa, wanda ke takarar dan majalisar wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birni da kewaye a jam’iyar PDP, ya ce manufar bada tallafin ita ce samar da ƙarin damar zuwa makaranta ga yaran da iyayensu ba su da karfin daukar nauyin karatun su.

A cewar sa, “babu yadda za a magance tarin matsalolin dake damun al’umar mu, ba tare da an samar da wata dama da yara zasu samu ilimi ba, ba tare da la’akari da nauyin aljihun iyayensu ba.”

“Allah ya sani ni dan talakawa ne kuma ina alfahari da damar da Allah ya bani ta taimaka wa al’uma, kuma babban buri na shine, yadda muka hadu a nan a ce bayan wasu shekaru an samu wasu daga cikin wadannan yara sun tara wasu ƴaƴan talakawa domin ɗaukar nauyin karatun su, ko da rai na ko babu.”

Ya ƙara da cewa, tun kafin ya fara neman takara ya fara kokarin taimaka wa ya’yan marasa karfi domin su samu ilimi kamar kowa.

Ya ce, “a baya mun ɗauki nauyin karatun ɗalibai da dama wajen rubuta jarabawar WAEC da NECO da kuma JAMB tsahon shekaru da suka wuce.”

“Hakan kuwa na da nasaba da nazari da muka yi akan alkaluma da ke nuni da cewa wani kaso mafi tsoka na dalibai kan hakura da cigaba da karatu saboda gazawa wajen samun kudin wadannan jarabawoyi, shiyasa muka dukufa wajen ganin cewa mun yi iya yin mu wajen tabbatar da cewa mun tallafi karatun dalibai da dama a fadin wannan karamar hukuma.”

Ya kuma kara da cewa nan gaba kaɗan zai sake ƙaddamar da shirin koyar da sana’o’in dogaro da kai ga mata da matasa, domin rage raɗaɗin tattalin arziki da ake fama da shi.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron, akwai tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa, Ghali Umar Na’abba da jigo a jam’iyyar PDP a nan Kano, Ibrahim Aminu Dan’iya da ma sauran manyan masu ruwa da tsaki na karamar hukumar birni da dama.