
Hassan Y.A. Malik
Hukumomi a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, a yau, Litinin, sun tabbatar da mutuwar dan wasan kungiyar mai buga mata baya, Chinedu Udoji, sakamakon wani mummunan hatsarin da ya rutsa da shi a daren jiya Lahadi.
Mai magana da yawun kungiyar, Idris Malikawa, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai, NAN wannan labari a Kano, inda ya bayyana cewa, Udoji ya gamu da hatsarin ne a kan hanyarsa ta dawowa daga ziyarar da ya kaiwa abokansa na tsohuwar kungiyarsa ta Eyimba da ke zaune a wani Otel a Kano bayan sun buga wasan Firimiya mako na 9 a yammacin jiya, inda aka tashi Kano Pillars 1-1 Eyimba.
Hadarin ya faru ne a kan titin Club Road, cikin birnin Kano, kuma tuni aka kai gawar Udoji asibintin Murtala aka ajeyeta a inda ake ajiye gawarwaki.
Zuwa yanzu dai, hukumomin Kano Pillars na jiran rahoton ‘yan sanda daga helikwatar ‘yan sanda ta Kano da ke Bompai game da hatsarin.
Udoji ne dan wasan da ya fi yin rawar gani a wasan da Kano Pillar ta buga da tsohuwar kungiyarsa, Eyimba jiya a Kano.