
Rashin halartar babban majistare, Abdulaziz Habib, a yau Litinin ya kawo tsaiko ga shari’ar wani dan siyasa mazaunin Kano, Abdulmajid Danbilki, wanda aka fi sani da Kwamanda, bisa zarginsa da tada zaune tsaye a lokacin wani shiri a gidan rediyo.
Ana tuhumar Danbilki da tada hankalin jama’a, wanda ya saɓa da sashe na 114 na dokar laifuka ta jihar Kano.
Da a yau za a yi zaman kotun domin yanke hukunci kan neman beli, wanda lauyan Kwamanda, Ibrahim Abdullahi Chedi ya gabatar a baya.
Ya bukaci kotun da ta bayar da belin wanda ake kara kamar yadda sashi na 35(5) da na 36 na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 da aka yi wa gyara ya tanada.
Sai dai kuma an ɗage shari’ar zuwa ranar 1 ga Maris, saboda rashin lafiyar alkalin.
“Ofishin ajiye bayanai ya sanar da mu yanzun nan cewa alkalin ba ya jin dadi kuma a halin yanzu yana asibiti,” in ji Chedi.
Lauyan mai gabatar da kara, Abdulsalam Saleh, na tuhumar wanda ake kara a wasu lokuta a cikin watan Janairu yayin da yake gabatar da wani shiri na rediyo da faifan bidiyo ya yi kira ga mazauna jihar Kano da su bijirewa duk wani yunkurin gwamnatin jihar na sake duba batun masarautar Kano.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
Hakan ne ya sanya aka dage sauraron ƙarar sai ranar 1 ga watan Maris, 2024.