
Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa, NERC, da Hukumar kula da Kadarorin Gwamnati, BPE, sun amince da naɗin Ahmed Dangana a matsayin Manajan- Daraktan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano, KEDCO.
Naɗin na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na kamfanin KEDCO, Ibrahim Sani Shawai ya sanyawa hannu a yau Alhamis.
Sanarwar ta ce amincewar ta biyo bayan sake fasalin 5 daga cikin Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki, DisCos da gwamnatin tarayya ta yi, sakamakon karɓe iko da guda 3 da Bankin Fidelity ya yi, wanda KEDCO na cikin su.
Shawai ya ƙara da cewa Dangana, kwararre ne a fannin bada shawarwari kan harkokin gudanarwa kuma yana da kwarewa kan harkokin kasuwanci, inda ya ce yanzu shine sabon shugaban kamfanin.
“Mr Dangana zai ɗora a kan nasarorin da aka samu a shugabancin da ya gabata don inganta ayyuka da kuma haɓɓakar tattalin arzikin kamfanin ta hanyar rage wasu kashe-kashe kudade da kuma inganta hanyoyin samun kuɗaɗen shiga,”