Home Labarai Danyen aiki: Ta sayar da janareton saurayinta ta sayi mayukan bilicin

Danyen aiki: Ta sayar da janareton saurayinta ta sayi mayukan bilicin

0
Danyen aiki: Ta sayar da janareton saurayinta ta sayi mayukan bilicin

Hassan YA Malik

An gurfanar da wata budurwa ‘yar kimanin shekaru 24 da haihu da aka bayyana sunanta da Bimpe Adeite a ranar Juma’ar da ta gabata, a gaban kotun majistare ta Badagry, Legas, bisa zarginta da sayar da janareton saurayinta da darajarsa ya kai N70,000 ba da izininsa ba, kana ta yi bukatun gabanta da kudin.

A cewar furosikyutan jami’an ‘yan sanda, Mista Akpan Uko, Bimpe ta aikata wannan danyen aiki ne a ranar 26 ga watan Janairu, 2018, a gida mai lamba 13, a kan titin Adamu da ke unguwar Itoga, a yankin Badagry.

Furosikyuta, ya ci gaba da cewa, janareton na saurayin Bimpe ne, mai suna Daniel Akanbi, wanda Bimpe kan ziyarta a dakinsa, su kuma kwashe lokaci tare.

Bimpe ta yi amfani da damar sanin lokacin da Daniel ba ya gida, inda ta shiga gidansa ta kinkimi janareton nasa ta kai wa ‘yan gwagwan, suka bata kudin, ita kuma ta kashe su akan gyaran gashi da karin gashi da kuma mayuka gyara fata.

Furosukyuta, ya bayyana wannan laifi na Bimpe da cewa, laifi ne wanda ke da hukunci a karkashin sashe na 285 na kundin laifuka na jihar Legas na shekarar 2011.

Sai dai kuma, Bimpe ta ki ta amsa laifinta, wanda hakan ya sanya Mai shari’a Jimoh Adefioye, ya dage sauraron karar zuwa ranar 1 ga watan Maris, tare da bada belin Bimpe akan kudi N100,000 da kuma wani wanda zai tsaya wa wacce a ke zargin, wanda kuma dole sai yana da shaidar biyan haraji ta jihar Legas.