
An kashe Darakta a Ma’aikatar kula da Ilimin Fasaha ta Ƙasa, NBTE, Abdu Isa Kofarmata, a harin da ƴan ta’adda su ka kai kan jirgin ƙasa da kar tahowa da ga Abuja zuwa Kaduna a jiya Litinin da yamma.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a harin, a na fargabar cewa ƴan ta’addan sun yi awon-gaba da fasinjojin, wasu kuma an kashe su, inda da dama su ka samu raunuka a harin.
Da ga cikin waɗanda su ka rasu har da Kofarmata, wanda wani ɗan uwansa ya ce ya rasu ne sakamakon harbin da yan ta’addan su ka yi.
A cewar sa, tuni a na kan hanya za a kawo gawar ta sa zuwa Jihar Kano domin a binne shi.
Ɗan uwan nasa ya ce marigayin, ɗan shekara 55, ya rasu ya bar mata ɗaya da ƴaƴa 4.