Home Siyasa Dattawan Arewa sun juya wa Atiku baya kan kalaman da ya yi na kar a zaɓi Beyerabe ko Inyamiri

Dattawan Arewa sun juya wa Atiku baya kan kalaman da ya yi na kar a zaɓi Beyerabe ko Inyamiri

0
Dattawan Arewa sun juya wa Atiku baya kan kalaman da ya yi na kar a zaɓi Beyerabe ko Inyamiri
Kwamitin hadin gwiwa na Arewa ya nisanta kansa daga kalaman ‘kada ku zabi Yarabawa da Igbo’ da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi a Kaduna a karshen mako.
Jaridar Punch ta rawaito cewa kwamitin, wanda ya hada da ƙungiyoyi daban-daban na ci gaban Arewa, da Jamiyyar Matan Arewa, ya ce ra’ayoyin da dukkanin ƴan takarar suka bayyana a taron nasu na mu’amala ne kawai.
“Ya kamata Atiku ya wanke kansa. Irin wannan tambayar da kwamitin ya yi an gudanar da ita ga sauran ‘yan takarar shugaban kasa su ma. Don haka, ba mu da wata alaka da ra’ayin da ba bakunan mu ne suka bayyana bs,” a cewar shugaban kwamitin gudanarwa na zaman, Murtala Aliyu, yayin da ya ke shaida wa manema labarai a Kaduna jiya.
Aliyu, wanda ya yi gargadin cewa “amfani da kabilanci da addini yana da matukar hadari ga siyasa,” ya bayyana damuwarsa cewa “Al’ummar kasar sun riga sun nuna alamun damuwa saboda wannan cin zarafi ne.”
Atiku ya yi haka ne a lokacin da yake amsa tambayar da Kakakin kungiyar dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba ya yi masa a kan dalilin da ya sa yake ganin ya kamata Arewa ta zabe shi a 2023, ya ce: “Matsakaicin dan Arewa ba ya bukatar shugaban Yarbawa ko Ibo, sai dai shugaban Arewa, wanda ya zama dan Najeriya.” in ji Atiku
Aliyu ya kuma yi taron manema labarai inda ya bukaci Atiku da ya kare kansa, ya kuma bayyana cewa ba a shirya mu’amala da ƴan takarar shugaban kasa ba domin goyon bayan ko daya daga cikinsu.
Ya ce babban burinsu shi ne jin ta bakin ’yan takarar yadda suka yi niyyar tunkarar kalubalen Arewa idan an zabi daya daga cikinsu a matsayin Shugaban kasa.
Bayanin na Atiku ya haifar da martani daga bangarori daban-daban tare da neman ya fito ya bada  hakuri
Sai dai kuma a ranar Litinin, mai taimaka wa Atiku kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya fayyace cewa ɗan takarar  ya fadi hakan ne cikin raha yayin mayar da martani ga wata tambaya da gaba daya ta shafi Arewa.
Ibe ya kara da cewa Atiku ba zai yi wani abu da bai dace ba don bukatarsa ta siyasa.