Home Siyasa Dauda Lawan ya sake samun tikitin takarar gwamna na PDP a Zamfara

Dauda Lawan ya sake samun tikitin takarar gwamna na PDP a Zamfara

0
Dauda Lawan ya sake samun tikitin takarar gwamna na PDP a Zamfara

 

 

Dauda Lawan Dare a jiya Juma’a ya sake samun tikitin takarar gwamna a jam’iyyar PDP, a Zamfara a 2023.

An sake zaben Mista Lawan Dare ne da kuri’u 422 a zaben-fidda gwani da wata babbar kotun tarayya da ke Gusau ta bayar da umarnin a yi.

Shugaban kwamitin zaben-fidda gwani na gwamna na jam’iyyar PDP, kuma shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, Hassan Hyet ne ya bayyana haka a karshen taron da aka gudanar a Gusau.

Hyet ya ce Lawan-Dare ya samu kuri’u 422 inda ya doke abokan hamayyarsa biyu da suka samu kuri’u ɗaya-ɗaya.

A cewarsa, daga cikin wakilai 431 da aka amince da su, 428 ne suka kaɗa kuri’ar inda ƙuri’u huɗu aka bayyana ba su da inganci.

Ya ce Dauda Lawan-Dare ya samu kuri’u 422, Ibrahim Shehu da Hafiz Nuhuche suka samu kuri’u ɗaya-ɗaya.

Ya ce: “Dr. Dauda Lawan-Dare, wanda ya samu kuri’u mafi yawa, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa a jihar Zamfara.”

Hyet ya yi nuni da cewa ɗaya daga cikin ƴan takarar Wadatau Madawaki ya janye daga takarar kafin a fara zaben.