
A jiya Alhamis ne mai shari’a Agatha Okeke na babbar kotun tarayya da ke Uyo a jihar Akwa Ibom ta yanke wa Albert Bassey, Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Gabas a majalisar dokoki, hukuncin daurin shekaru 42 a gidan yari.
Kotun ta same shi da laifuka shida na karkatar da kudade da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta shigar a kansa.
EFCC ta gurfanar da Sanata Bassey a gaban kuliya bisa zargin karbar motoci da darajarsu ta kai Naira miliyan 204 daga wasu kamfanoni da ke da alaka da wani dan kwangila mai suna Olajide Omokore.
Omokore dai ya aiwatar da kwangilar Naira biliyan 3 ga gwamnatin jihar Akwa Ibom, lokacin Sanata Bassey ya na kwamishinan kudi, kuma shugaban kwamitin kula da ayyukan ma’aikatu na kai-tsaye.
Laifin ya ci karo da Sashe na 15 (2) (d) na Dokar Hana Kudade, 2011 (kamar yadda aka yi masa kwaskwarima) kuma akwai hukunci shi a karkashin sashe na 15 (3) na wannan dokar.