Home Labarai Ku dena siyan magungunan gargajiya, NAFDAC ta gargaɗi ƴan Nijeriya

Ku dena siyan magungunan gargajiya, NAFDAC ta gargaɗi ƴan Nijeriya

0
Ku dena siyan magungunan gargajiya, NAFDAC ta gargaɗi ƴan Nijeriya

 

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa, NAFDAC ta sake yin gargaɗi ga ƴan Nijeriya da su dena sayen haɗe-haɗen magungunan gargajiya a gurin ƴan talla saboda ba su da ingantaccen wajen ajiya.

Darakta-Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta yi gargaɗin a yayin tattaunawa ta musamman da Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Legas a yau Laraba.

Darakta-Janar ɗin ta yi gargaɗi da a guji duk wani magani da ake tallan sa a gefen titina, kwararo-kwararo da cikin motocin haya sabo da rashin tabbacin in da a ka yi shi.

“irin magungunan nan na ganje-gaje, in dai ya yi kwana 4 ko 5 zai fara fitar da ƙwayoyin cutar bacteria.

“To ko da waɗannan na ɗauke da wasu sinadarai na magani, to wannan bacteria ɗin ce za ta kashe wanda ya ke shan maganin,” in ji ta.

Adeyey ta ƙara da cewa wasu magungunan gargajiya ɗin su na aiki, amma sai sun tabbatar da cewa sai sun tsallake gwajin NAFDAC.