
Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bukaci ƴan Najeriya da su ci gaba da nuna tausayawa, kulawa, kauna, da kuma tallafa wa masu fama da cutar kansa da wadanda suka warke da ga cutar.
Misis Tinubu, a cikin sakonta da ta fitar a jiya Lahadi don bikin ranar tunawa da masu cutar daji ta duniya, ta jaddada bukatar kara dagewa wajen bunƙasa fannin lafiya domin samar da ingantacciyar kulawa ga masu fama da cutar kansa da wadanda su ka warke.
Ta ce: “Ranar cutar kansa ta duniya ta wannan shekara tana ba da muhimmiyar dama don wayar da kan jama’a tare da kara fayyace saƙon rigakafi, gano cutar da wuri, da kuma maganin cutar ta kansa.
“Ba za mu zuba ido mu kyale masu fama da kalubalen cutar kansa kadai ba. Mu ci gaba da nuna tausayi, kulawa, ƙauna, da goyon baya ga masu fama da ciwon da waɗanda suka warke, duk da cewa muna ƙara wayar da kan jama’a da shawarwari don samun kulawa mai inganci.
“Har ila yau, mu na yin barka ga waɗanda ba su da cutar kansa.”