
Dillalan man fetur a Nijeriya sun rubuta wasikar koke ga shugaban ƙasa Bola Tinubu cewa karya farashin dizel zuwa Naira 900 duk lita da matatar mai ta Dangote ta yi na yin illa ga kasuwancinsu.
Devakumar Edwin, mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta shafin X wacce Nairametrics ta shirya.
“Dillalan man fetur a Nijeriya sun rubuta wasika ga shugaban ƙasa Tinubu domin yin korafi kan cewa farashin man dizel a matatar mu ya yi kasa daga 1200 zuwa 1000 a yayin da yanzu ya kara karye wa zuwa 900 duk lita wanda hakan yake shafar kasuwanci su”,inji shi.
Edwin ya bayyana wasu daga cikin kalubale da matatar man ta Dangote ke fuskanta da kuma tasirinta ga man da ƙasar nan ke samarwa da kuma farashi.
Acewarsa, matatar wacce ke unguwar Lekki a jihar Legas, na ta fafutukar siyar da tanka 29 na Dizel a duk rana sakamakon ƙarancin siyan man daga ƴan kasuwar gida.
“Sakamakon wannan ƙarancin siyan man daga ƴan kasuwar gida, matatar ta fitar da mafi yawancin man dizel da na jirgin sama zuwa ƙasashen waje”, inji shi.
Tun da farko, Edwin ya ce matatar man zata dinga fitar da shi waje idan kamfanin NNPCL ya ƙi siya.
“Muna fitar da man jiragen sama, muna samar da Kalanzir”.
Edwin ya kuma bayyana mamakin sa kan yadda matatar ta fara samun kalubale a yayin da ta shirya fara aiki.