Home Labarai Direban babur ɗin adaidaitasahu ya gudu da taliya katan ɗaya a Kano

Direban babur ɗin adaidaitasahu ya gudu da taliya katan ɗaya a Kano

0
Direban babur ɗin adaidaitasahu ya gudu da taliya katan ɗaya a Kano

 

 

 

Wani matuƙin babur mai ƙafa uku, wanda ake kira da adaidaitasahu a Jihar Kano ya tsere da katan ɗin taliya, mallakar wani ɗan kasuwa, Muhammad Auwal.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tun da fari, Auwal ya sayo katan 30 na taliya a kasuwar Singer domin kaiwa ga wani mutum a unguwar Brigade, sai ya kira mai adaidaitasahu domin yai masa dakon kayan.

A cewar Auwal, da yayi niyyar baiwa ɗan adaidaitasahu ɗin lambar mai kayan ya kai masa, inda ya ƙara da cewa da ya kira shi bai daga ba, sai ya shiga motarsa, ya kuma tasa direban adaidaitasahu ɗin a gaba zuwa wajen mai kayan.

KARANTA: Gwamnatin Kano ta hana yin hayar adaidaita sahu daga ƙarfe 10 na dare

Sai dai kuma ko da a ka isa wajen sauke kayan, a cewar Auwal, sai direban adaidaitasahun ya faki ido ya sauke katan 29 a maimakon 30, ya kuma tsere da guda ɗaya.

“Gaskiya ban ji daɗi ba saboda shi direban adaidaitasahun nan ya ci amana. Shi yasa mu ke ganin ba daidai ba a ƙasar nan sabo da muna zaluntar junan mu.

“Na taso shi a gaba ni kuma ina cikin mota. Ko da mu ka isa inda zai sauke kayan, da ya fuskanci hankali na ya yi wani wajen, sai ya faki ido na ya gudu da katan ɗaya, gaskiya ban ji daɗi ba,” in ji shi.

A makon da ya gabata ne dai Gwamnatin Jihar Kano ta hana matuƙa adaidaitasahun yin aiki daga ƙarfe 10 na dare zuwa ƙarfe 7 na safe.