
Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wani direban tankar mai, Ɗahiru Aliyu, a defon NNPC da ke Hotoro, a Jihar Kano.
Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da safe.
“Mun samu kiran kar-ta-kwana da ga wani Shu’aibu Muhammad da misalin 10:59 na safe. Nan da nan mu ka tura dakarun mu wajen,” in ji Kakakin.
Abdullahi ya baiyana cewa marigayin, ɗan shekara 45, ya shiga cikin tankin ne da bokiti da kuma ruwan kumfa domin ya wawanke nason da fetur ya yi a jikin tankin, amma sai ya ja iska ya kuma ce ga garinku nan.
Abdullahi ya ƙara da cewa lambar rijistar tankar itace DKD 411 XF.