
Ƙungiyar masu motocin haya ta intanet na gudanar da zanga-zanga a yau a Abuja bayan sun gudanar da yajin aiki na kwana uku.
Yaƴan ƙungiyar na National Coalition of ride sharing professional NACORP waɗanda akasarinsu masu aiki ne da kamfanin sufuri na Bolt da Uber na zanga-zangar ne bisa wasu ƙorafe-ƙorafe.
Ɗaya daga cikin ƙorafe-ƙorafen har da son kamfanin Bolt da Uber su kara rage kason da suke yanka daga kuɗin fasinjojin da suke jigila.
Haka kuma suna ƙorafin cewa an sha kashe direbobinsu kan hanya ba tare da kamfanin Uber ko Bolt sun ɗauki wani mataki ba.