
A tabbatar da dokar hana acaɓa a Jihar Legas, gwamnatin jihar ta niƙe babura 2,000 da ta kama sakamakon karya dokar.
Gwamnatin jihar dai ta hana yin acaɓa a Ƙananan Hukumomi shida da kuma gundumomi tara na jihar da ga 1 ga watan Yuni.
Kwamishinan Sufuri na jihar, Frederic Oladeinde ne ya baiyana haka a wata sanarwa a Legas.
Ya kuma jaddada ƙoƙarin gwamnatin na kare rayuka da dukiyoyi.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Gbenga Omotoso, yayin taron manema labarai a kan niƙe baburan a Ikeja ya baiyana cewa hakan ya nuna cewa gwamnati ba za ta janye dokar ba.
Omotoso ya ƙara da cewa a halin yanzu an kai mutane 21 kotu sakamakon karya dokar, inda a ka kwace baburan sama da dubu biyu
Ya ce ƴan acaɓar da a ka hana yin hayar, idan su na da buƙata, su ne aikin tukin motocin haya na Mil ɗin farko da na ƙarshe, inda ya ƙara da cewa za a kawo motocin domin ɗabbaƙa hana acaɓar.
Ya ce ƴan acaɓa a Ƙananan Hukumomin da a ka hana ka iya zuwa su shiga cibiyoyin koyon sanar hannu 18 da gwamnati ta samar a faɗin jihar.
Ya kuma yaba wa al’umma da dama bisa yin biyayya ga dokar.