
Haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, a yau Laraba, ta bukaci mazauna Kudu-maso-Gabas da su fara binne gawarwakinsu cikin kwanaki uku.
A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar ta IPOB, Emma Powerful, wacce jaridar Daily Post ta samu, IPOB ta yi zargin cewa ɗabi’ar ajiye gawarwaki a ɗakin ajiye gawa na tsawon lokaci ne ya haddasa wasu kalubalen da ke fuskantar Kudu-maso-Gabas.
Kungiyar ta bukaci ƴan kabilar Igbo da su koma ga tsohon salon binne gawawwakinsu, inda ta ce idan ba haka ba to za ta sanya a rufe ɗakunan ajiye gawarwaki a yankin Kudu-maso-Gabas.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ta duniya da kuma iyalan masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) a karkashin jagorancin Mazi Nnamdi Okwuchukwu Kanu na fatan sanar da daukacin ƴan Biafra, abokan Biafra da kuma masu son fafutukar neman kafa kasar Biafra cewa lokaci ya yi da ƴan Biafra da su fara binne mamata cikin kwanaki uku kamar yadda ake yi a zamanin da.
“Kakanninmu suna binne matattu cikin kwana uku, kuma al’adunmu ke nan, kuma hakan ya taimaki kakanninmu a rayuwarsu. Igbo suna da al’adu masu arziƙi da ruhi waɗanda kakanninmu suka kiyaye tun farkon zamani,”