Home Labarai Dole masu motocin haya da na gida su yi amfani da na’urar ƙayyade gudu — FRSC

Dole masu motocin haya da na gida su yi amfani da na’urar ƙayyade gudu — FRSC

0
Dole masu motocin haya da na gida su yi amfani da na’urar ƙayyade gudu — FRSC
PIC. 25. AN ACCIDENT SCENE ON MILLENNIUM PARK ROAD IN ABUJA ON TUESDAY (27/1/13).

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa, FRSC, reshen jihar Ogun a jiya Laraba a Abeokuta, ta ce amfani da na’urar takaita gudu abin-hawa ya zama tilas ga motocin haya da na gida.

Anthony Uga, Kwamandan Hukumar ta FRSC a Ogun, ya ce a yayin taron ƙarawa juna ilimi na zango na ɗaya na 2024 kan hanyoyin rage haɗurra a kasar nan.

Uga ya lura da cewa gudun-wuce-sa’a ya janyo sama da kashi 90 cikin 100 na hadurran ababen hawa (RTCs) a jihar.

“Na’urar da ke kayyade gudu tana nan daram saboda na’urar ta na cetar rayuka da dama,” in ji shi, inda ya bukaci masu ababen hawa da su bi ka’idojin na’urar.

Kwamandan sashin ya bayyana cewa hukumar ta FRSC za ta fara aiwatar da tsauraran matakai kan tursasa amfani da na’urar.