Home Labarai Dubarudun tattalin arziki Buhari da cancantar zaben Atiku

Dubarudun tattalin arziki Buhari da cancantar zaben Atiku

0
Dubarudun tattalin arziki Buhari da cancantar zaben Atiku

Fassarar Rubutun Ilyasu Ibrahim

January 22, 2019

Ba sai an nanata ba, sanin duk wani xan Nijeriya ne cewa tun bayan zaven 2015, kuma bayan xarewar Shugaban qasa Muhammadu Buhari bisa karagar mulki abubuwa da dama, musamman waxanda suka shafi tattalin arziki sun sukurkuce, talakawa suka rasa tudun dafawa. Haka kuma idan aka koma kan batun tsaro, wanda yana xaya daga cikin maqusadan kowace irin gwamnati da ke mulki wato ta kare dukiyoyi da rayukan al’umma daga faxawa cikin tsaka mai wuya nan ma ba ta canza zane ba, domin kuwa gwamnati mai ci yanzu ta faxi qasa warwas, kuma har yanzu batun da ake, ta gaza tashi ballantana ma ta kakkave qasar da  ke gwuyawunta.

To amma ko dama Hausawa sun ce duk wanda ya sayi rariya ya san tilas za ta zubar da ruwa. Kowa ya san dagar da aka sha da Buhari da gwamnatinsa a can baya, wato zamanin mulkin sojoji, sai ga shi duk da cewa yanzu gwamnatin ta dimokuraxiyya ce, amma kamar jiya, i yau, tamkar ungulu ta koma gidanta na tsamiya ne. Za a iya gane haka daga ire-iren qorafe-qorafen da al’umma ke yi a kan gazawar gwamnatin Buhari, musamman ma na kusa da shi da suka haxa har da matarsa, za a iya bada tabbacin cewa gwamnatin ta bai wa maraxa kunya kuma ba ta da wata alqibla da za ta iya fuskanta ko da kuwa Shugaban qasa Buhari zai yi mulki shekara dubu, annabi dada.

Ba zai yiwu a iya kattaba ire-iren gazawar shugaban qasa Buhari da gwamnatinsa ba, amma babba da kowa na ji a jikinsa ita ce ta fannin tattalin arziki. Ba sai an nanata ba, gwamnati kowace iri ce ita ke da alhakin tsara manufofinta na tattalin arzikin qasa, waxannan manufofi kuma su ke jan ragamar al’amurran ci gaban qasa, amma ita gwamnatin Buhari saboda gwanancewarta, ita ce aka tava yi da ba ta da gwanin ko masanin tattalin arzikin a cikin masu gudanar da mulkin qasa. Wannan ba komi ya nuna ba sai gwamnati ce da ba kai, ba gindi, kuma shi ne ya kai qasar nan da talakawa cikin halin qunci da talauci da ke damuwarta.

Ai tamkar xa ne da iyayensa suka nuna wa so suka shagwava shi, don haka tilas ya yi abin da ya ga dama, ba tare da shakku ba ko damuwa da halin qunci da wasu ke ciki.

Saboda haka muddin al’amurran tattalin arziki suka tavarvare a qasa tilas a samu matsaloli na tashin-tashina ko rikice-rikice ko da kuwa al’ummar ta cika ta tumbatsa da masana da ‘yan boko, ba za su tava samun damar kai wa ga gaci a matsayinsu na masu tunani da hangen nesa ba, ko da kuwa suna da wadatattun kayan aiki, muddin babu tsayayyen tsari na tattalin arziki da zai yi masu jagora, shirim ba ci ba ne ai!

Wani abin takaicin ban tausayi kuwa (wai matar maye ta mutu bai ci ba) shi ne, gwamnatin shugaba Buhari ta kasa hango mafita duk da kasancewar madubin dubarudu a tafin hannunta yake, sai ma dai qara tavarvarcewa da ta yi a harkokin tattalin arziki wanda a kullum ya ke kwan-gaba-kwan-baya. Babban qalubalen da irin rashin sanin makama kan jawo shi ne, yakan kawo lalacewar tattalin arziki, kuma abu ne mai matuqar wuya kafin a gano bakin zaren nan take. Haka zalika hakan ya yi tasiri ga miliyoyin ‘yan Najeriya duk da kuwa irin halin juriya da qulafucin da suke nuna wa shugaba Buhari.

Alal misali, idan muka dubi batun hanyoyin sadarwa na zamani. Gwamnatin shugaba Buhari ce ta umurci kamfanoni sadarwa da su qara farashin kuxaxin sayen tsarin data. Har wa yau gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emelife, ya qara jaddada cewa duk wani kiran waya ko sadarwa da ta wuce minti uku to tilas a xaga farashin kiran. Ba hauhawar farsashin tsarin sadarwa na kafafen sadarwa ne kaxai ya zamo wa ‘ya Najeriya qadangaren baki tulu ba, uwa uba har da hauhawar da kayan albarkatun mai suka yi, wanda  hakan shi ya haddasa tashin gwauron zabin da kayan masarufi suka yi a  kasuwanninmu, da suka haxa da kayan albarkatun noma, kamar shinkafa da takin zamani da dai sauran su. Babu ko tantama gwamnatin ta yi haka ne ba don ciyar da qasa gaba ba sai don buxe wata kafa ta satar kuxaxe wajen gudanar da harkokin tafiyar da jam’iyar da ke mulki.

Da wannan sabon tsari musamman na tsadar data da tsarin kafafen sadarwa, talakan Nijeriya tilas ya gwammace yin awon hatsi a maimakon sayen katin waya ko tsarin data, don haka ba zai samu damar amayar da ra’ayinsa ba ko nuna damuwa ko qorafinsa ta waxannan kafafen sadarwar. Wannan ma wani sabon tsari ne na mulkin kama karya da gwamnatin shugaba Buhari ta shimfixa cikin ruwan sanyi, ba tare da talakan Najeriya ya ankara ba. Wata tambayar da ya kamata mu yi kawunanmu kuwa ita ce, shin bayan waxannan hanyoyin karvar haraji da gwamnati mai ci yanzu ta bijiro da su, nan gaba kuma waxanne hanyoyin za ta sake zaqulowa, wata qila ma titunan da muke bi za mu fara biya wa haraji ko ma iskar da muke shaqa, kai hatta gonakinmu da muka gada kaka-da-kakkani ma sai mun biya masu haraji?

Wata qila ma shi ya sa wani shehun malami mazaunin qasar Amurka yake da ra’ayin cewa gwamnatin shugaba Buhari gwamnati ce ta jari hujja, haka zalika duk ginin da aka aza da jari hujja to tamkar an yi gini ne da toka. Wannan shi ke ba wasu miyagun shugabanni ko ‘yan siyasa kafa don su lalata tattalin arzikin tare da yin babakere kan wasu muhimman muqamai suna ci da gumin talakawa. Hasali ma, wannan ne ya sa Hausawa kan ce sai bango ya tsage qadangare kan samu wurin shiga.

Ga gwamnatin Buhari, jefa tattalin cikin halin ni ‘ya su bai isa ba, su a gurin su husufin da tattalin arzikin qasa ya shiga hanya ce ta jefa ‘ya Nijeriya a cikin sabon tasku, shi ya qara bai wa gwamnatin damar sauya akalar tunani ‘yan qasa, a kullum qaryarsa ita ce an sha wahala kafin a sami biyan buqata, tir da irin wannan batu nasu. A maimakon gwamnati ta ji qan talakawa da saka masu shauqi a cikin zukatansu a lokacin da tattalin arziki ke cikin tsaka mai wuya, sai ya buxe kafa ga wasu miyagun shugabanni a cikin gwamnati mai ci yanzu, suna qara jefa talakawa cikin qunci da damuwa.

Da a ce gwamnatin shugaba Buhari mai hangen nesa ce, da ta  hango waxannan matsaloli a matsayin damarmakin da za ta nuna tausayawarta ga ‘yan Nijeriya; amma sai ga shi kuma aka sami akasin haka. Haka zalika wani sakarcin da gwamnatin ta nuna shi ne na rashin tausaya wa ga talakan Nijeriya, ta yadda suka yi qoqarin xaga darajar naira, amma kuma haqarsu ba ta cimma ruwa ba. Gwamnatin shugaba Buhari ta shafe tsawon shekara xaya cikin halin husufin tattalin arzikin qasar kafin ta farga da cewa qudirin nata ba zai yiwu ba a cikin wannan qarnin da muke ciki na 21. Sun bar naira na ta tamvele ba tare da sun samar mata mazauni ba, saboda yadda suka kasa suka tsare game da yadda suke so darajar naira ta kasance a kasuwannin duniya. Wannan sakaci nasu shi ya ba da dama ga cin hanci da rashawa da almundahana suka yi ta cin karensu ba babbaka tsakanin kasuwannin canjin kuxaxe.

Daga baya ne suka shafa wa ‘yan canji kashi kaji, suka kai wa kasuwannin canji farmaki. Daga wannan lokaci ne darajar naira ta faxi warwas, ‘yan canji suka shiga cin kasuwannin bayan fage. Wannan ya  qara haifar da tumbatsar faxuwar darajar naira. Bugu da qari, sanin kowa ne cewa matsi da takura ba shi zai sa a samu sauqin xaga darajar naira ba, hasali ma shi ke qara haifar da kangara da turjiya daga ma su hada-hadar cinikayyar, musamman ta bayan fage.

Wani batun kuma shi ne ta vangaren albarkatun noma. Gwamnatin shugaba Buhari ta bakin ministan albarkatun noma Audu  Ogbeh, ya bayyana cewa suna niyyar su sake dawo da tsohon tsarin nan na hukumomin qayyade farashin albarkatun noma. An koma gidan jiya ke nan, wai dabara ta qare wa makaxi.

Ba sai an nanata ba gwamnatin shugaba Buhari, gwamnati ce da ke qudurin mai da wa ‘yan Nijeriya hannun agogo baya, maimakon ta fuskanci matsalolin rashin guraben ayyukan yi ga matasa, wanda a kullum ake ta faman rasa aikin yi ga matasa. Wani abin mamaki ma shi ne yadda gwamnatin ta umurci hukumar qididdiga da ta qididdige yawan marasa aikin yi, wanda hakan ma shigar burtu ne da gwamnatin ke yi wa ‘ya qasa don ta voye gazawarta.

Babu ko tantama muddin aka sake bai wa gwamnatin shugaba Buhari damar sake zarcewa a zaven 2019, shakka babu ‘yan Nijeriya za su qara shiga cikin halin qunci da ba tava ji ko gani ba

Saboda haka muke ganin lokaci ya yi da za a sake lale, a nemi irin su Alhaji Atiku Abubakar wanda ya taka muhimmiyar rawa, mussaman ta vangaren hulxar kasuwanci, don haka shi ne mafi cancanta ga zaven 2019, idan aka yi la’akari da nasarorin da ya samu, wanda hakan ke nuni da cewa yana da kyakyawan qudiri da hangen nesa wajen farfaxo da tattalin arzikin qasa. Alhaji Atiku mutum ne da ke da yaqinin cewa al’umma a kowane mataki kan iya ceto kanta daga tavarvarewar arziki, don haka ya dage tuquru wajen taimakon matasa don su tsaya da duga-dugansu, haka zalika ya yi imanin cewa gwamnati tana da irin tata rawar da za ta taka wajen warware matsalolin tattalin arziki musamman ganin cewa ‘yan Nijeriya mutane ne da ke da saurin karvar canje-canjen da za su iya kawo sauyi da zai yi tasiri a rayukansu  cikin walwala, don haka a shirye yake don ya bada irin tasa gudunmuwar wajen havvaka tattalin arzikin qasar Nijeriya. 

Ilyasu Ibrahim ya rubuta daga Abuja