
Hukumar kula da Zirga-zirgar Jiragen sama ta Ƙasa, NCAA, a yau Juma’a ta tabbatar wa matafiya cewa jiragen da ke jigila a ƙasar lafiyayyu.
Darakta-Janar na hukumar, Kaftin Musa Nuhu ne ya baiyana haka a yayin taron shekara-shekara karo na 46 da Kungiyar Hukumomin Tafiye-tafiye ta Ƙasa, NANTA, da ya gudana a Kano.
Nuhu ya ce ya yi wannan bayanin ne domin ya ƙaryata batun da yawancin matafiya ke faɗi cewa kamfanonin jiragen sama na ƙasa su na sayo tsofaffin jirage.
Sai dai kuma ya yi kira da masu ruwa da tsaki a ɓangaren sufurin samada su mayar da hankali kan yin aiki tare domin ci gaban masana’antar.