
Uwar Jam’iyar PDP ta ƙasa ta sa ƙafa ta shure umarnin da kotu ta bata na kada ta rushe shugabannin jam’iyar na Jihar Kano, inda ta sauke shugabancin tun da ga matakin mazaɓa har zuwa matakin jiha.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a yau Talata ne Babbar Kotun Taraiya a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Taiwo O. Taiwo ta dakatar da PDP din da ga rushe shugabancin jam’iyar a Kano har sai ta gama jin ƙarar da aka shigar a gabanta.
Sai dai kuma PDP ɗin, a wata sanarwa da Sakataren Tsare-tsaren ta, Umar M. Bature ya fitar a yau Talata, ya baiyana cewa an rushe shugabancin jam’iyar bayan tattaunawa da kuma nazari a kan hakan, duba da yanayin da jam’iyar ta shiga a jihar.
A cewar Bature, rushe shugabancin jam’iyar ya yi daidai da tanadin sashi na 29(2)(b) da 31(2)(e ) na jam’iyar.
Ya ƙara da cewa tuni ma PDP ɗin ta amince da naɗa shugabannin riƙon ƙwarya da za su ci gaba da riƙe jam’iyar har tsawon kwanaki 90, kamar yadda sashi na 24(2) na jam’iyar, wanda a ka yi masa garambawul a 2017 ya tanada.
Ya ce kwamitin rikon kwaryar ya haɗa da ;
Alhaji Ibrahim Atta — Shugaba
Alhaji Ibrahim Aminu Dan’Iya — Mamba
Hajiya Ladidi Dangalan — Mamba
Hon. Aminu Abdullahi Jungau — Mamba
Mukhtar Mustapha Janguza — Mamba
Abdullahi Isa Sulaiman — Mamba
Barr. Baba Lawan — Mamba/Sakatare