
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce duk sanda ya ji an ambaci haruffan jam’iyar PDP, ba abinda ya ke zuwa ran sa sai matsala.
Buhari ya baiyana hakan a yayin tattaunawa ta musamman da gidan talabijin na Channels TV a jiya Laraba.
Ɗaya da ga cikin masu tambayoyin, Maupe Ogun ya cewa Buhari ce “abinda za mu tambaye ka a ka yi mana shine ka fada mana abinda ke zuwa maka a rai idan ka ji waɗannan kalmomi. Ka faɗa mana a cikin jumla ɗaya kawai.
Siɗira ta farko a kan matasan Nijeriya ce.
Sai Buhari ya amsa da cewa “ina fatan idan su ka je makaranta, su ka yi ƙoƙari, su ka kammala digiri ɗin su, kar su jira sai gwamnati ta basu aiki.
“Sabo da mai ilimi ya fi maras ilimi ko a wajen ma fitar da matsaloli. Sabo da haka ilimi ba yana nufin gwamnati ta baka aiki ba, kamar yadda turawan mulkin mallaka su ka saka mana a zuƙatan mu. Shine ka mallaki mota, ka tafi ofis ƙarfe 8 sannan ka tashi karfe 2,”
Sai ɗaya mai tambayar, Seun Okinbaloye shima ya ɗora da tashi tambayar cewa “ɗaya kalmar ita ce PDP, mai ya ke zuwa maka a rai idan ka ji PDP?”
Sai Buhari ya bada taƙaitacciyar amsa da cewa “PDP matsala.”