
Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ce masu sukarsa kan ɗaukar Kashim Shettima a matsayin mataimakin dan takara a zaɓen 2023, sun tuntuɓe shi domin neman wannan mukami.
Ya ce akasari mukasanta ne a gareshi, sannan ya ce sun nuna sha’awar ya zaɓe su, wanda yaƙi amincewa da hakan.
Tinubu na waɗannan kalamai ne a lokacin tattauna wa da shugabannin kungiyar kiristoci ta CAN a Nijeriya.
Ya shaida wa shigabann CAN ɗin cewa ba don addini ya zaɓi Shettima s matsayin mataimakin takararsa ba sai dan cancantar sa.
Zaɓin da Tinubu ya yi wa Shettima, ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin masu ganin takarar ta zama ta musulmi zalla.
Wadanda suka caccaki zaɓin sun hada da Babashir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya wanda kuma makusanci ne ga Tinubun.
Akwai kuma tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara da shi ma ya nuna akwai rashin dacewa a hada musulmi da musulmi takara.