
Ɗan majalisar Tarayya Mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Tarauni a Majalisar wakilai, Hafizu Kawu Tarauni ya nemi afuwar duk wanda ya ɓata wa ko ya yi masa laifi, bisa kuskure.
Kawu ya nemi afuwar ne a wani taron manema labarai da ya kira a Kano a jiya Asabar, inda ya ce shi ya yafe wa kowa.
Ɗan majalisar ya kuma ce lokaci ya yi da al’umma za su fahimci cancantar wanda ya kamata ya wakilce su a majalisar kasa domin samun ci gaba mai ɗorewa.
Hafizu Kawu ya ce tsawon shekarun da su ka gabata ta wakilcinsa a majalisa ya samar da ayyukan ci gaba daban daban-daban a yankinsa, inda ya ƙara da cewa ya sama wa matasa ayyukan yi.
Ya ƙara da cewa ya bada gagarumar gudummawa a ɓangaren ilimi da koyar da sana’oi, har ma da bada jari ga mata da matasa.
Hafiz Kawu ya ce akwai wasu manyan ayyukan na nan tafe kafin ƙarshen wa’adinsa, musamman ga yankunan da ayyukan basu je gare su ba.
Ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Tarauni da su sake bashi dama a zaɓe mai zuwa inda zaici gaba da kawo wa yankin kaɓakin arziki.
Kazalika yaja hankalin matasa da su guji siyasar daba da ta’ammali da miyagun kwayoyi, inda ya lura da cewa hakan ke mai dasu baya wajen inganta cigaban rayuwarsu.
Ya ƙara da cewar duba da rawar da mata ke takawa a sha’anin zaɓuka, hakan ta sa ya yi musu tsari na musamman da zai tallafi rayuwarsu tare da cigaba da samar masu da jari domin dogaro da kai.
Daganan Dlɗan majalisar ya yi addu’ar dorewar zaman lafiya a jihar Kano da ma kasa baki daya tare da neman afuwar duk wani wanda yake ganin an bata masa domin cigaban jam’iyyar APC a kakar zaɓe mai zuwa.