
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi barazanar hukunta duk waɗanda aka kama su na aikata munanan ɗabi’u a wannan wata mai tsarki na Ramadana.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Lawan ya fitar ranar Alhamis a Kano.
Ya ce Shugaban na Hisbah, Dakta Harun Ibn-Sina ya bayyana cewa wadanda suke aikata munanan dabi’u a cikin wannan wata mai alfarma, za a yi maganinsu.
“Wasu daga cikin matasan da ke cin abinci a bainar jama’a a lokacin azumi su ma ba za su tsira ba,” inji shi.
Malam Ibn-Sina ya yi kira ga jama’a da su taimaka wa marayu da mabukata, a wani yunkuri na ba da taimako ga radadin da suke ciki.
Ya kuma bayyana cewa Hisbah za ta tura jami’anta zuwa masallatai domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a cikin watan Ramadan.
Babban kwamandan hukumar, ya ce: “Rundunar Hisbah za ta ziyarci masallatai a lokutan buda baki, Tarawihi, Sallar Tahajjud domin kare masu ibada da dukiyoyinsu daga rashin kishin kasa.