Home Labarai Duk wani gini da aka yi ba bisa ƙa’ida ba, ko na wanene sai na rushe shi — Ministan Abuja, Wike

Duk wani gini da aka yi ba bisa ƙa’ida ba, ko na wanene sai na rushe shi — Ministan Abuja, Wike

0
Duk wani gini da aka yi ba bisa ƙa’ida ba, ko na wanene sai na rushe shi — Ministan Abuja, Wike

Sabon Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi barazanar rushe duk wasu gine-gine da aka yi ba bisa ƙa’ida ba da ke lalata tsarin babban birnin tarayya.

Ministan ya yi wannan gargadin ne a jawabinsa na farko bayan ya tare a ofishin hukumar babban birnin tarayya, FCTA a yau Litinin, jim kadan bayan rantsar da su da shugaba Bola Tinubu ya yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Tsohon Gwamnan Jihar Rivers ɗin na tare da Mariya Mahmud, Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya, ya ce: “Duk wadanda ke lalata tsarin Abuja, abin ya yi muni.

“Idan kun san kun yi gini a inda bai kamata ku yi gini ba, to kuwa zan sauke shi,” in ji Wike yayin wani taron manema labarai a Abuja a yau Litinin, jim kadan bayan rantsar da shi a fadar gwamnati,”

Ya kara da cewa duk wanda ya yi gini a inda bai kamata ba, ko da mai laifin minista ne ko ambasada, “dole ne mu sauke ginin ka”.

Ya kuma gargadi masu mallakar filaye da suka mamaye “wuraren shike-shuke” da gine-gine, yana mai cewa tilas ne wuraren su dawo yadda su ke a da.