
Kwamitin Shirya Gasar Wasanni ta Jami’o’i, NUGA, ya cimma matsaya da Kungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa, ASUU da ke yajin aiki domin yin gasar ta 2022 kamar yadda a ka tsara.
Sakataren shirya gasar ta 2022, Joseph Awoyinfa, shi ne ya baiyana haka ga manema labarai a yau Talata a Jihar Legas.
Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa Jami’ar Legas ce za ta karɓi gasar da za a fara a ranar 16 ga watan Maris a kuma kammala a ranar 26 ga watan na Maris.
Ya ce a ƙalla ƴan wasa da jagororin su 10,000 da ga jami’o’i 136 a ke tsammanin za su shiga gasar mai ɗauke da wasanni daban-daban har guda 17.
Awoyinfa ya tabbatar da cewa yakin aikin da ASUU ta je yi ba zai kawo naƙasu a gasar ba, inda ya ƙara da cewa kungiyar ce ma ta sahale da bada makonni uku domin yin gasar.