Home Labarai EFCC ta kama Akanta-Janar Ahmed Idris kan badaƙalar naira biliyan 80

EFCC ta kama Akanta-Janar Ahmed Idris kan badaƙalar naira biliyan 80

0
EFCC ta kama Akanta-Janar Ahmed Idris kan badaƙalar naira biliyan 80

 

 

 

Jami’an Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa ta Ƙasa, EFCC, a jiya Litinin su ka kama Akanta-Janar na Ƙasa, AGF, Ahmed Idris, bisa zargin karkatar da kuɗaɗe da kuma almundahana da su ka kai Naira biliyan 80.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar, ta tabbatar da cewa bayanan sirri da hukumar ta samu sun nuna cewa AGF ya mallaki kuɗaɗen ne ta hanyar yin kayi-nayi na ƙarya da sauran ayyukan da suka saɓawa doka ta hanyar amfani da ‘yan uwa, iyali da abokai makusanta.

An karkatar da kudaden ne ta hanyar zuba su a harkar gine-gine a Kano da Abuja.

An kama Idris ne bayan ya kasa amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa na amsa batutuwan da suka shafi ayyukan zamba.