
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin Arzikin Kasa ta’annati EFCC, ta kama Shugaban majalisar dokokin Jihar Ogun, Olakunle Oluomo.
Jami’an hukumar ta EFCC sun kama Shugaban majalisar ne ranar Alhamis da misalin karfe 9 na safe a filin Jirgin Sama na Murtala Mohammed dake Jihar Legas.
Gidan talabijin na Channels ya tawaito cewa jami’an EFCC sun kama Dan majalisar dokokin ne domin ya amsa musu wasu tambayoyi dake da alaka da almundahanar kudade.
Shugabancin hukumar kawo yanzu basu ce komai akan lamarin ba, Amma dai ana sa ran zasu fitar da sanarwa nan bada jimawa ba.
Wata majiya dake da alaka da hukumar EFCC ta bayyana cewa, hukumar ta gayyaci Kakakin majalisar lokuta da dama amma ya gaza amsa kiranta.
Yanzu haka dai sun tafi da Oluomo zuwa ofisoshin hukumar ta EFCC dake Lagos domin Yi masa wasu tambayoyi.
Yanzu haka dai majalisar dokokin jihar Ogun hankali ya kwanta bayan da jami’an hukumar ta EFCC suka kama Kakakin majalisar.
Duk da al’amarin ya lafa, har yanzu dai kofar da ake shiga harabar majalisar na nan a rufe, yayin da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya wato Civil Defense suka yi wa kofar shiga tsinke.
Hakazalika, an hana shiga harabar majalisar yayin da masu ziyarar da ke ciki da wajen majalisar suka koma baya.