Home Labarai EFCC na neman tsohon Minista ruwa a jallo

EFCC na neman tsohon Minista ruwa a jallo

0
EFCC na neman tsohon Minista ruwa a jallo

Hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa, EFCC, ta bayyana cewa ta na neman tsohon Ministan Wutar Lantarki da Karafa, Olu Agunloye bisa zargin almundahana da yin karyar takardu.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun kakakinta, Dele Oyewale, kuma ta wallafa a shafukan Facebook da Instagram na hukumar a yau Laraba.

“Ana sanar da jama’a cewa Dokta Olu Agunloye, wanda hotonsa ya bayyana a sama, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) na neman sa ruwa a jallo bisa zargin almundahana da ƙaryar takardu.

“Hukumar EFCC na neman Dr Olu Agunloye. Idan kun san inda yake, don Allah kar ku yi kasa a gwiwa ku sanar da EFCC ko ofishin ƴansanda mafi kusa,” in ji shi.

A cewar hukumar, Agunloye mai shekaru 75, ya fito ne daga karamar hukumar Akoko ta Arewa a jihar Ondo.

Har ila yau, ta bayar da adireshinsa na karshe mai lamba 20, Solel Boneh Way Bodija, Ibadan, Jihar Oyo.

Hukumar EFCC ta bukaci duk wanda yake da cikakken bayani game da inda yake da ya tuntubi ofisoshinta da ke Benin, Kaduna, Ibadan, Sokoto, Maiduguri, Makurdi, Ilorin, Enugu, Kano, Lagos, Gombe, Uyo, Fatakwal da Abuja, ko kuma ta layukan ta da kuma ta wayar tarho. imel.

A baya dai hukumar ta gayyaci Agunloye domin amsa tambayoyi kan rawar da ya taka a kwangilar samar da wutar lantarki ta Mambila na dala biliyan shida.