
Daga Hassan Y.A. Malik
Dailypost ta rawaito cewa Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya yi kira ga likitocin jihar kaduna da su yi gaggawar duba lafiyar kwakwalwar gwamnan jihar, gwamna Nasiru El-rufai bisa ga irin kalaman da ya ke furtawa na rashin hankali.
Sanatan ya bayyana hakan ne ta wata wasikar da ya rubutawa babban daraktan asibitin masu fama da matsalar kwakwalwa ta jihar Kaduna a ranar 7 ga watan Mayu, inda ya ce, gwamnan na bukatar ganin likitan mahaukata.
Shehu Sani ya bayyana mamakinsa ta yadda za a yi gwamna guda wanda shine tsaro alummar jiharsa ta rataya a kansa ke tunzura jama’ar zuwa ga tashe tashen hankula da rikici saboda harkokin siyasa.
Sanatan ya kara yin kira da a binciken kalaman gwamnan da wata kila yana fama da wata matsalar kwalkwalwar wanda jama’a basu sani ba.