
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahamed ElRufai ya bayyana ta hannun mai magana da shi Samuel Aruwan cewar an sassauta dokar hana fita a wasu yankunan jihar Kaduna yayin da aka samu rahotannin samun Zaman lafiya a yankunan.
Sai dai kuma sanarwar sassauta doka ta bayyana cewar akwai unguwannin da har yanzu suke karkashin dokar hana shiga da fita ta tsawon awa 24, yankunan da wannan doka ta Shata su ne Narayi da Kabala ta kudu da Kabalan doki da saban tasha.
Banda wadannan yankuna an sassauta dokar zuwa 5 na safe zuwa 6 na maraice a dukkan sassan cikin garin Kaduna da kewaye.