
Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Mai horar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG, Unai Emery ya mayarwa da kungiyoyin real Madrid da Barcelona da Bayern munich martini bisa zargin kungiyarsa da su ke yi na tana kashe kudi ba bisa ka’ida ba wajen siyan ’yan wasa.
A tattaunawarsa da manema labarai a shirye-shiryen da kungiyarsa take na fafatawa da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich a gasar zakarun turai a jiya laraba, Emery yace kishi ne kawai yake damun qungiyoyin ba wani abu ba.
Ya ce lokacin da yake kungiyar kwallon kafa ta Sevilla ta kasar Spaniya yana ganin yadda Real Madrid da Barcelona da Barcelona da Manchester da City da Juventus su ke kashe kudi wajen siyan manyan yan wasa masu tsada amma babu wanda ya daga kai ya yi magana.
Ya kara da cewa yanzu ana ganin kungiyarsa ta shiga sahun manyan kungiyoyi a duniya wadanda zasu iya fafatawa da kowacce kungiya shi ne yasa ake musu wannan kallon.
A karshe ya ce yanzu abin farin cikine a wajensu ace duk duniya ana magana akan PSG inda ya ce wannan ba karamin cigaba ba ne kuma suna nan za su ci gaba da siyen manyan yan wasa domin gogawa da manyan kungiyoyi.