
Manajan tantance labaran ƙarya na kamfanin Facebook, reshen Yankin Gabas-ta-Tsakiya, Afirka da da ƙasar Turkiyya, Tom Nvumba-O’Bryan, ya bayyana cewa sun cire shafuka da labarai sama da miliyan 18 waɗanda ke yaɗa labaran ƙarya kan cutar Korona daga dandalin Facebook.
Mr. Nvumba-O’Bryan ya baiyana hakan ne lokacin da ya ke jawabi kan hanyoyin amfani da fasaha wajen yaƙi da yaɗa labaran ƙarya a wani taro da aka yi a Abuja.
DUBAWA ce ta shirya taron na wuni biyu, wanda ke da burin hada kan ‘Yan jarida, malaman makarantu, masu bincike da ma jama’a baki daya wajen tattauna matsalolin da ke tattare da yada labaran karya da ma irin yinkurin da ake yi na dakile irin haka.
Mr Nvumba-O’Bryan ya ce kamfanin Facebook wanda yanzu ake kira Meta Platforms, Inc, yana amfani da matakai uku wajen tantance labaran karya kamar haka: Ragewa, cirewa da sanarwa.
Ya ce: “Daya daga cikin dalilan da ya sa muke abota da kungiyoyin da ke tabbatar da sahihanci labarai shi ne irin taimakon da mu ke samu wajen tantance labaran karya da yin watsi wadanda ba su da tushe.”