Home Labarai Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata rahoton da a ke zargin SSS sun rubuta kan takarar Musulmi-da-Musulmi

Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata rahoton da a ke zargin SSS sun rubuta kan takarar Musulmi-da-Musulmi

0
Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata rahoton da a ke zargin SSS sun rubuta kan takarar Musulmi-da-Musulmi

 

 

Fadar shugaban kasa ta ce babu wani rahoto na sirri kan da a ke zargin hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, ta gabatar wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a kan tikitin takarar shugabancin ƙasa na Musulmi-da-musulmi na jam’iyar APC a zaɓen 2023.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, ya bayar da rahoton cewa, wata jarida ta yanar gizo, Peoples Gazette, a jiya Juma’a ta rawaito daga rahoton na SSS, cewa hukumar ta fusata kan shawarar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC (Bola Tinubu) ya yanke na tsayar da dan uwansa ​​Musulmi a matsayin mataimakin takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Jaridar ta yanar gizo ta kuma ruwaito rahoton yana bayyana matakin na Tinubu a matsayin wani mataki na sabon rikicin kabilanci da zai iya dagula zaman lafiyar Najeriya.

Ta kuma ƙara da cewa, hukumar SSS ta aikewa shugaba Buhari wani rahoto na sirri, wanda ke nuni da illolin tsaro na zaben tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa ga Tinubu.

“Takardar, wacce ta samu shugaban kasa ta hannun mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ta ce ya kamata yayi Tinubu ya yi la’akari da illar zaɓen da ya yi kafin ya bayyana shi a fili,” inji jaridar.

Sai dai, Garba Shehu, mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, a wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a a Abuja, ya bayyana rahoton ta yanar gizo a matsayin na ƙarya don nufin haifar da rarrabuwar kai da hargitsi kan zaɓin na Shettima.

Shehu, don haka ya shawarci ƴan kasa da su riƙa yin watsi da abin da ya bayyana a matsayin rahotanni gurɓatattu, inda ya kira jaridar ta yanar gizo a matsayin “kwayar cuta mai saurin kisa”.