Home Labarai Fadar Shugaban kasa ta kira Kwankwaso da Ganduje domin sasantawa

Fadar Shugaban kasa ta kira Kwankwaso da Ganduje domin sasantawa

0
Fadar Shugaban kasa ta kira Kwankwaso da Ganduje domin sasantawa
Abdullahi Umar Ganduje

Bayan da Sanata Kwankwaso ya yarda ya jingine batun zuwansa Kano a ranar talata, fadar Shugaban kasa a ranar liinin ta yi wani kiran gaggawa tsakanin Kwankwaso da Ganduje domin magance yamutsi a jihar kano.

Gwamna Ganduje ya isa fadar Shugaban kasa bisa rakiyar wasu Sanatoci guda biyu tare da wasu ‘yan majalisar tarayya guda biyu, ya kuma gana da Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa, Malam Abba Kyari.

Mista Ganduje bai yarda yayi magana da ‘yan jarida ba a yayin da ya fito daga ganawar da suka yi da Malam Abba Kyari a fadar ta shugaban kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar, ana sa ran nan gaba a yau shima tsohon Gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai gana da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo.

NAN ta habarto cewar, wannan ziyara da Kwankwason ke son kaiwa Kano ta dumama hazo da yawa, inda mutane da dama suke kiraye kirayen kada yaje kano a wannan lokacin domin gudun zuar da jini.

Haka nan, shi kansa, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Rabiu Yusuf ya shawarci Sanata Kwankwaso akan kada ya shigo Kano a wannan lokaci da al’amura suka dau dumi dangane da ziyarar tasa.

Duk da waccan shawara da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, rabiu Yusuf ya baiwa Kwankwaso, amma ya ce zuwansa kano babu gudu babu ja da baya.

NAN