
Fafaroma Francis ya yi kira ga Shugaban Ƙasar Russia, Vladimir Putin da ya ji tsoron Allah ya dena wannan “kisan l-ƙare-dangin” a Ukraine.
Fafaroma ya yi gargaɗi cewa idan a ka ci gaba da haka to garuruwan Ukraine za su zama maƙabarta.
Ya ce “dole a daina wannan kisan da a ke yi wa Ukraine da muggan makamai,”
Da ya ke jawabi a huɗubarsa ta ranar Lahadi, Fafaroma ya suffanta da cewa “ta’addanci” ne, jefa bamabamai kan asibitocin yara da sauran al’umma, inda ya ce “basu da wata hujja ta yin hakan”.