Home Ƙasashen waje Fafaroma ya zargi wasu malaman coci da kallon batsa a intanet

Fafaroma ya zargi wasu malaman coci da kallon batsa a intanet

0
Fafaroma ya zargi wasu malaman coci da kallon batsa a intanet

 

Fafaroma Francis ya yarda cewa akwai malaman coci maza da mata da ke kallon hotunan batsa ta intanet.

A kan haka ya gargade su cewa yin haka abu ne mai hadari.

Shugaban mabiya addinin Kiristan ya ce babu wani nau’in hoton batsa da addini ya yadda a kalla.

A cewarsa ta hakan ne shaiɗan ke samun kafar shiga jikinsu ya karya zuciyoyinsu.