Home Labarai Fafutikar ‘yan NEPU ce ta sanya talaka yake samun mukami a yau – Sule Lamido

Fafutikar ‘yan NEPU ce ta sanya talaka yake samun mukami a yau – Sule Lamido

0
Fafutikar ‘yan NEPU ce ta sanya talaka yake samun mukami a yau – Sule Lamido

 

Tsohon Gwamanan jihar Jigawa kuma tsohon ministan harkokin kasashen wajen na Najeriya, Alhaji Sule Lamido, mai son zama shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP a 2019, sannan daya daga cikin samarin NEPU a wancan zamani na Jamhuriya ta Farko kuma wanda da shi a ka kafa jam’iyyar PRP ta Marigayi Malam Aminu Kano, ya bayyana cewa, duk wani dan talaka da a ka zaba a mukamin siyasa tun daga kan shugaban kasa har zuwa kansila ya ci gajiyar ’Yan NEPU ne, wadanda su ka sadaukar da rayuwarsu.

Ya ce, ’Yan NEPU ne su ka yi wannan sadaukarwa da rayukansu da ’yancinsu, domin talaka ya zama ya samu ’yanci na ya yi karatun boko a duk wani fanni da ya ke so kuma har ya samu damar shiga siyasa a zabe shi a kowanne mukami na siyasa kamar ’yan majalisar dattawa da na wakilai da ma na jihohi har ma da kujerar shugaban kasa, gwamna, shugaban karamar hukuma, saboda albarkacin gwagwarmaya ’Yan NEPU da a ka azabtar a ka kashe wasu, wasu su ka yi gudun hijira duk don ’yanci ya samu ga talaka a siyasar Nijeriya.

Sule Lamido ya bayyana haka ne ga manema labarai a ranar tunawa da addu’o’in da a ka yiwa jagoran NEPU da PRP Marigayi Malam Aminu Kano, wanda ya cika shekaru 35 da rasuwa da a ka gabatar a gidan tunawa da Malam Aminu Kano a Mumbayya House da ke unguwar Gwammaja cikin Birnin Kano. Lamido ya ce, “yau dan talaka ne ya ke aikin likita, ya ke aikin lauya, ya ke aikin alkali, ya ke aikin jarida da dai sauran ayyuka na kamfanoni da harkar kasuwanci da shahara a kowanne fanni ba tare ka ji an ce jikan sarki wane ba ne ko dan sarki wane ba ne.

Ashe kuwa ’yanci ya samu ya ga dan talaka. Da ma kuma shi ne babban burin akidar NEPU da ita PRP da a ka kafa ta a shekarar 1978 bayan an dade da kafa jam’iyyar NEPU, wacce Malam Aminu Kano ya jagoranta don fafutikar kwato ’yanci daga hannun sarakuna.” Ya cigaba da cewa, “tarihi ba zai manta ba da irin azabar da a ka gana wa ’Yan NEPU irin su Malam Lawan Dambazau, Alhaji Babba Dan Agundi, Alhaji Lili Gabari, Gambo Sawaba, Haruna Danjani, Ila Ringim, Musa Guza Namamuda da dai sauran manya manyan ’Yan NEPU da su ka fuskanci azaba iri-iri a kan akidarsu ta NEPU.

Wasu har kashe su an yi, an daure wasu, saboda a tozarta su duk da kasancewar su mutane ne mawadata masu ilimin addini da duk wata daraja da dan adam ya ke bukata, amma hakan bai hana azabtar da su ba.” Dangane da maganar da a ke yi yanzu na cewa ’ya’yan talakan ne a mulki kuma su na azabtar da talakawa, ya ce, “wannan maye ne da tumbudi na ’yanci da ya samu ’ya’yan talaka. Saboda haka ko ba komai ’ya’yan talaka ne dai ke azabtar da talaka kuma wato kuma wannan wani abu ne wanda ya ke mai zaman kansa, amma da a ce ba talaka ba ne da talaka, to da shi ma wani abu ne daban. Amma dai adalci shi ne akidar NEPU ta zo da shi ba zalunci ba.” Haka kuma ya ce, “duk dan NEPU da PRP ana gane shi ne ta hanyar yin aiki tukuru na gina al’umma, domin wannan ce ta sa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, ya yi aiki tukuru. Ko ya na so ko ba ya so, haka zai yi.

Haka shi ma Marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi shi ma haka ce ta sa ya yi aiki a Kano da Jigawa da a ke ta mamaki, inda ko aikin da a ka gani a ke cewa Alhaji Sule Lamido ya yi wa Jigawa aiki, to shi ma wannan dalili ne na NEPU da PRP, domin idan ba ka yi aikin ba, to ka bata tarihin NEPU da PRP kuma ka baddala manufarta. To, kuwa dan NEPU da PRP na hakika ba zai yarda ya kashe tarihin NEPU da PRP ba. Don haka idan na zama shugaban kasa haka zan yi aiki.”

Dangane da taro da a ka yi na jam’iyyarsa ta PDP a Jigawa, Katsina da ma duk inda a ka yi taron PDP, ya ce, “ya cika wani abu ne mai zaman kansa na cewa yanzu babu jahilci babu dole babu tsoro. Zamani ne na kafofen sadarwa iri-iri na zamani kuma mutane su ne alkalan kansu. Idan sun zabi halin da a ke ciki na kashe-kashe da rashin tsaro da fatara da yunwa da a ke ciki a yanzu, to shikenan ’yancinsu ne, damarsu ce su zabi abinda su ke ganin ya dace da su, domin kamar ka samu kudi ne ka ga duk abin da ka yi, kudinka ne, amma fa ka sani idan ka sabawa Allah, kudinka ne, amma ka san fa ka yi ba daidai ba kuma ya na nan a rubuce; za ka ga abinda ka yi a nan gaba.”

Haka kuma a karshe Alhaji Sule Lamido ya nuna takaicinsa na cewa, Najeriya ita ce uwar kasashen bakaken fata na duniya, amma abin takaici yau a wannan taro na tunawa da Malam Aminu Kano a nan ne a ke ba da misalin cigaba da kasar Ruwanda da Ghana su ka yi, ba a na maganar cigaban Najeriya ba.