
Kwamishinan Shari’a na Jihar Kwara, Salman Jawando ya yi zargin cewa “a na ɗebe kuɗaɗen gwamnati bayan fakewa da cewa dole a bayar da kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane sannan su saki waɗanda su ka kama.”
Jawando ya yi wannan zargi ne a ranar Litinin a yayin taron ranar Shari’a na 2021/2022 da kuma bikin sallamar alaƙalan da su ka yi murabus da ga aiki a Ilori.
Jawando ya bi sahun waɗanda su ke kira da a yi wa ɗaukacin fannin Shari’a garambawul a Nijeriya.
“Rashin tsaro a ƙasar nan ya yi ƙamari har ta kai ga ba wan da ya ke yin Bacci da ido biyu a rufe,” in ji shi.
“Batun kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane ya zamo wata hanya 5a samun maƙudan kuɗaɗe da ɓatagari su ke yi da haɗin kan wasu mugayen mutane.
“Ya zamo wata hanya da a ke kwashe kuɗaɗen gwamnati inda a ke fakewa da biyan kuɗin fansa da ƙaryar cewa wai idan ba a biya ba to waɗanda a ka sace ɗin za su shiga uku.
“Ɓangaren Shari’a wanda ya zamana nan ne madogarar talaka a ƙasar nan ya kamata ya tashi ya yi tashi tsaye domin tserar da ƴan ƙasa da ga wannan bala’in da ke cinye tsokokin jikkunan mu,” in ji Jawando.
Kwamishinan ya nuna mamaki da yadda a ke jan ƙafa a shari’ar masu garkuwa da mutane, inda ya baiyana cewa hakan na nuni da cewa dole a yi garambawul a gaba ɗaya ɓangaren Shari’a a ƙasar nan.