Home Labarai An fara kiraye-kiraye na a dakatar da batun sake fasalin Naira

An fara kiraye-kiraye na a dakatar da batun sake fasalin Naira

0
An fara kiraye-kiraye na a dakatar da batun sake fasalin Naira

 

Wata kungiya mai suna Concerned Northern Forum, ta yi kira da a dakatar da canza fasalin takardar kudi, nai 200, N500 da 1000, inda ta ce matakin zai yi illa ga tattalin arzikin kasa.

Babban bankin Najeriya CBN, ya sanar da cewa zai sake fasalin takardar kudi daga ranar 15 ga watan Disamba.

Da yake mayar da martani ta wata sanarwa a yau Alhamis a Kaduna, mai magana da yawun kungiyar, Abdulsalam Kazeem, ya ce sake fasalin zai yi wa darajar Naira illa.

Ya bayyana cewa sun yi kira da a dakatar da ƙudurin ne duba da cewa farashin Naira zuwa dala ko fam, ya sanya Naira ta rasa darajarta.

Ya yi kira da a samar da manyan tsare-tsare na tattalin arziki da za su karfafa Naira idan aka kwatanta da dala da fam.

Mai magana da yawun kungiyar ya ce tattalin arzikin Najeriya ya karye, kuma darajar Naira ta yi kasa sosai, don haka sake fasalin takardun kudin zai jawo wa gwamnati asarar makudan kuɗaɗe kuma kuɗaɗen talakawa za a diba a yi aikin.
.