Home Labarai Farashin abinci na ci gaba da tashin gwauron zabi a Abuja

Farashin abinci na ci gaba da tashin gwauron zabi a Abuja

0
Farashin abinci na ci gaba da tashin gwauron zabi a Abuja

 

Farashin kayan abinci na ci gaba da tashi gwauron zabi a Abuja da jihar Nasarawa, inji rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN.

Wani bincike da NAN ta gudanar ya nuna cewa a Nasarawa da babban birnin tarayya, mazauna garin na cikin takaici saboda karin farashin kayan abinci.

Wani ɗan kasuwa a kasuwar Kubwa, Dini Suleiman ya ce a baya ana sayar da buhun wake kan Naira 27,000 amma yanzu a na sayar da shi kan Naira 49,000.

Suleiman ya ce a baya ana sayar da buhun shinkafar yar gida tsakanin N15,000 zuwa N20,000, inda ya ce a yanzu ana sayar da shi kan Naira 29,000, yayin da buhun shinkafar ƙasar waje da ake sayar da ita kan Naira 25,000 yanzu ta koma N34,000.

Buhun garri mai launin rawaya, wanda aka sayar akan N8,000, a halin yanzu ana sayar da ita kan N22,000 yayin da farar garri da aka sayar akan N6,000 a halin yanzu ana sayar da shi akan N17,000.

Suleiman ya ce buhun masara a baya ana sayar da shi kan N6,000 yanzu ya koma N20,000.

Ya alakanta hauhawar farashin kayan abinci da tsadar sufuri, wanda ya ce hakan ya shafi karfin saye, wanda hakan ya sa farashin kayan abinci ya tashi.