
A karon farko tun bayan soma yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine, farashin alkama a kasuwannin duniya ya sakko sosai.
Dukkan kasashen sun sanya hannu kan yarjejeniya a jiya Juma’a inda aka amince cewa za a ci gaba da fitar da hatsi ta tekun Black Sea wanda Rasha ta toshe tsawon watanni.
Rebecca Grin Span, wadda babbar sakatariya a Majalisar Ɗinkin Duniya ce kan cinikayya da kuma raya kasa na da cikin jagorori a yarjejeniyar da aka cimma.
Ta ce wannan yarjejeniya ce kwarai da gaske da ta shafi duniya, saboda za ta shafi miliyoyin mutane musamman wadanda ke a kasashe masu tasowa.
BBC Hausa ta rawaito Shugaban Ukraine Volodymyr Zekensky, ya ce fitar da tan miliyan 20 na hatsi zai taimaka wajen kauce wa fadawa gagarumar matsalar karancin abinci a duniya.