
Farashin biredi ya ƙaru a jihar Benin, in ji Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN.
Binciken da NAN ya gudanar ya nuna cewa an samu ƙarin farashin ne sakamakon tashin farashin garin alkama, wanda shi ne babban sinadarin da ake amfani da shi wajen noman biredi.
A binciken da NAN ya yi, akwai yiyuwar farashin biredi zai ci gaba tashi a Nijeriya nan da makonni masu zuwa.
Wannan ya faru ne sakamakon ƙarancin samar da alkama a duniya sakamakon yakin Russia/Ukrain da ke gudana.
Binciken da NAN ya yi a wajen wasu masu sayar da biredi a ranar Alhamis a Benin sun ga cewa karamin biredi da aka sayar da shi kan N120 a watan Nuwamba 2021, yanzu ana sayar da shi N180.
“Matsakaicin biredi da ake sayar da shi kan Naira 300 watanni bakwai da suka wuce, yanzu ana sayar da shi a kan Naira 450, yayin da babban biredi ake sayar da shi a kan N850, sabanin N500 da ake sayar da shi a watan Nuwamba 2021,”