Home Cinikayya Farashin gangar mai ya haura zuwa $80 a kasuwar duniya

Farashin gangar mai ya haura zuwa $80 a kasuwar duniya

0
Farashin gangar mai ya haura zuwa $80 a kasuwar duniya

Farashin gangar danyen mai ya haura zuwa dalar Amurka 80 a karon farko tun cikin watan Disambar 2014. Wannan haurawa da farashin yayi ta faru ne bayan da masu lura damanyan ma’ajiyar mai ta kasar Amurka ta bayyana cewar man da Amurkan ke da shi yayi kasa sosai.

Fitowar wannan bayani ke da wuya, farashin gangar danyen man ya haura. Tun dai a watan Disambar shekarar 2014 rabon da gangar danyen man tayi wannan tashin gwaron zabin.

Sai dai tun a kwaar farko ta wannan shekarar ne aka fashimci raguwar man dake ma’ajiyar dan yen mai ta kasar Amurka, man dai ya tashi da kashi 60 daga asalin yadda yake a da.

Tun kusan farkon Shekarar 2016 ne kasar ta Amurka ta kara adadin yawan man da take saya daga kasashen duniya da kashi 16.

Kasar Saudiyya ce dai tafi kowacce kasa samun garabar fitar da adadin man fetur a tsakanin kasashen da ke da albarkatun man a dukkan kasashen duniya.