Home Kasuwanci Farashin Gas din girki ya ragu a Najeriya – Gwamnati

Farashin Gas din girki ya ragu a Najeriya – Gwamnati

0
Farashin Gas din girki ya ragu a Najeriya – Gwamnati

 

Gwamnatin tarayya ta ce ta na daukar matakan da su ka dace, domin ganin an kara rage farashin iskar Gas din da a ka fi sani da gas din girki.

Gwamnati ta bayyana hakan ne yayin da ta ke mayar da martani ga raguwar farashin iskar gas a kwanan baya.

Bincike ya nuna cewa farashin iskar gas mai nauyin kilo 12.5 ya ragu da ga Naira 8,800 zuwa tsakanin N8400 zuwa N8200.

A wasu shagunan farashin ya ragu zuwa tsakanin Naira 7,800 zuwa N8,000 a ranar Alhamis.

A watan Nuwamba, farashin gas ya tashi sama da kashi 240 tsakanin Janairu da Oktobar 2021.

Farashin ya ƙaru da kashi 240 a kan kilo 12.5, inda ya tashi daga Naira 3,000 zuwa Naira 10,200 a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2021.

Kimanin kashi 65 cikin 100 na LPG a na shigo da su Najeriya ne, yayin da abin da a ke nomawa a cikin gida ya kai kashi 35 cikin 100, domin haka farashin kayayyaki a kasuwannin duniya ya shafi farashin cikin gida.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adeshina ya ce farashin gas na duniya ya yi tashin gwauron zabi a cikin watan Oktoban bara, amma ya ragu zuwa karshen shekarar 2021 zuwa watan Janairun 2022, wanda hakan kuma ya taimaka wajen faduwar farashin nasa a fadin ƙasar nan.