Home Labarai 2023: Mu na farautar wasu ƴan siyasa — EFCC

2023: Mu na farautar wasu ƴan siyasa — EFCC

0
2023: Mu na farautar wasu ƴan siyasa — EFCC

 

Yayin da aka fara yakin neman zaben 2023, Shugaban Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa hukumar ta baza komar ta a kan wasu ƴan siyasa.

Bawa ya bayyana haka ne a jiya Talata a Legas yayin wani taron bita na kwana ɗaya kan rahoto kan laifukan harkokin kuɗi da hukumar ta shirya wa wasu ƴan jarida.

A cewarsa, hukumar ta kuma mai da hankali sosai kan ayyukan wasu lauyoyi, dillalan motoci, dillalan gidaje, dillalan duwatsu masu daraja, akawu, da kamfanonin gine-gine da dai sauransu.

Shugaban na EFCC ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa wadannan harkokin sun zama wata hanya ta satar kudade.

Don haka shugaban hukumar ya bukaci ƴan jarida da su san sabuwar dokar kudaden haram domin su san yadda za su rika rahoto a kai da kuma taimakawa wajen ilimantar da sauran ƴan kasa.

“Na tabbata yawancin mu muna sane da sauye-sauyen da ƴan majalisa su ka kawo da ya haifar da dokar laifukan harkokin kuɗi ta 2022.

“Akwai wasu tanade-tanade na wannan sabuwar doka da na yi imanin za su shafe ku kai tsaye ko ta wata hanyar. Daya shine sirrin hada-hadar kudi.

“Sabuwar dokar ta haramta gudanar da asusu masu lamba sannan kuma ta umarci cibiyoyin kudi da su tantance masu amfani da asusun kafin bude irin wadannan asusu,” in ji shi.