
A jiya Asabar ne jihar Borno ta yi bikin cika shekaru 62 da samun ƴancin ancin kai a Nijeriya, inda aka gudanar da fareti a dandalin Ramat da ke Maiduguri, wanda shi ne na farko cikin shekaru 12 tun fara rikicin Boko Haram.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Usman Kadafur, ya yabawa rundunar soji da sauran jami’an tsaro kan irin gagaruman nasarorin da aka samu wajen yaƙi da ƴan ta’adda.
Ya ce taron ya samu ne bayan dawowar zaman lafiya a jihar.
Gwamnan ya ce nasarorin da aka samu a yaki da ta’addancin ya baiwa gwamnatin jihar damar rufe dukkanin sansanonin ƴan gudun hijira a Maiduguri da Ƙaramar Hukumar Jere.
Ya bayyana cewa yawancin mutanen da su ka rasa matsugunan su ne bisa radin kansu sun koma garuruwa da kauyukansu.
Gwamnan ya ce aikin da ke gaban gwamnati shi ne sake gina muhimman ababen more rayuwa da aka lalata a cikin shekaru 12 da aka shafe ana tada kayar baya.
“Mun sabunta alkawarinmu na tunkarar kalubalen muhimman ababen more rayuwa da rikicin Boko Haram ya lalata tsawon shekaru goma.
“Da kuma binciko hanyoyin samar da guraben ayyukan yi ga matasa marasa aikin yi, ta yadda za a rage yawaitar munanan dabi’u a cikin al’umma.
“Muna da yakinin cewa tare da dimbin jarin da muka yi a cikin shekaru uku da suka gabata wajen fadadawa da karfafa ayyukan sake tsugunar da mu da kuma farfado da mu, za mu yi nasara a kan kudurinmu na samar da ribar dimokuradiyya,” in ji shi.